Daga ibrahim Musa kallah

Kwamishinan muhalli na jihar katsina Alh Musa Adamu funtua ya jadadda kudirin Gwamnatin jihar katsina don ganin bunkasa aiyyukan ci gaba a jihar katsina

Musa Adamu funtua ya bayyana haka ne a tattaunawar da sukayi da wakilinmu a ofishinsa dake katsina

Ya bayyana cewa babban manufar wannan Gwamnati ne taga cewa ta gina Al,umar jihar katsina don ganin inganta rayuwarsu da duk taimakon daya dace.ta fannoni daban daban.

Musa Adamu yace Yana daga cikin dalilian da yasa Gwamna malam Dikko radda a lokacin campaign ya zagaya kananan hukumomi talatin da hudu 34 don gano matsalolinsu da hanyoyin daza a magancesu musamman Sha,anin tsaro Wanda shine na farko a wajen wannan Gwamnatin domin maganceshi don samun ingantaccen zaman lafiya Mai dorewa a jihar da yardar Allah.

Da yake bayani ta fuskar Sha,anin muhalli.
Kwamishinan muhallin Musa Adamu yayi alwashin aiki tukuru da gaskiya don samun kyakkyawan muhalli don inganta rayuwar alumar jihar katsina baki daya .

Musa Adamu funtua yace daga hawansa kwamishinan muhalli ya zagaya ma,aikatun dake karkashin ma,aikatarsa domin gani da idonsa, da Jin matsalolinsu don magancesu ta yanda za a tafiyar da aiki cikin nasara.

Yayi kira ga daukacin Al,umar jihar katsina dasu kula sosai wajen tsabtace muhalinsu da kwalbatocinsu domin samun ingantaccen kiwon lafiya a tare dasu.

Ya bayyana cewa Gwamnati bazata Yi kasa a guiwa ba domin daukar matakin daya dace ga masu sare saren itatuwa ba bisa kaida ba.
Ya Kuma nemi jama,a dasu ci gaba da goyawa Gwamnatin malam Dikko radda baya domin kawo aiyyukan ci gaba a jihar ta katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here